Gwamnonin arewa maso yamma za su haɗa kai wajen bunƙasa noma da magance matsalar tsaro

Gwamnonin yankin arewa maso yamma sun amince su yi aiki tare wajen magance matsalar tsaro da kuma bunƙasa aikin gona a yankin.

Gwamnonin sun dauki wannan matsaya ne biyo bayan wani taro da suka yi ranar Talata a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara, Ahmed Aliyu gwamnan jihar Sokoto, gwamnan Kebbi, Nasir Idris da kuma mataimakin gwamnan jihar Jigawa Aminu Usman sai kuma mai masaukin baƙi gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya bayyana cewa gwamnonin sun faɗi cewa yin aiki tare shi ne zai amfani yankin.

Ya ce dukkanin gwamnonin sun amince su yi aiki tare wajen inganta fannin noma ta hanyar samar da kayan aiki da kuma kasuwannin hada-hadar kayan abinci.

More News

Wani mutumi ya yi garkuwa tare da kashe ƴar’uwarsa a Kaduna

A ranar Lahadin ne mazauna birnin Zariya na jihar Kaduna suka shiga alhini cikin alhini sakamakon kama wani mai suna AbdulAzeez Idris da ake...

Ɗan ta’addar Boko Haram ya miƙa kansa ga sojoji

Alhaji Wosai wani mamba a ƙungiyar ƴan ta'addar Boko Haram ya miƙa kansa ga dakarun sojan Najeriya na rundunar Operation Haɗin Kai. Rahotanni sun bayyana...

An kuɓutar da wasu ɗaliban da aka sace a jami’a a Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa an ceto 14 daga cikin daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Osara Okene...

Hukumar NMDPRA ta rufe wani gidan mai da ya karkatar da tankar man fetur 18

Hukumar NMDPRA dake lura da tacewa tare rarraba man fetur da iskar gas ta rufe gidan man Botoson Oil and Gas LTD dake jihar...