Gwamnatin Zamfara ta umarci jami’an tsaro su harbe masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya umarci jami’an tsaro da su dauki tsattsauran mataki kan mutanen da suke aikin haÆ™ar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.

A wata sanarwa ranar Asabar, mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris ya ce tsawon shekaru hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba na ruruta wutar rikicin yan bindiga da kuma sauran ayyukan laifi a jihar.

A cewar mai magana da yawun gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen ayyukan haÆ™ar ma’adanan tare da aiwatar da matakan da za su kare lafiyar al’umma.

A saboda haka aka umarci jami’an tsaro da su yi ta maza su harbe duk wanda aka samu da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

“Umarnin ya zama dole domin kare lafiya da tsaron al’ummar jihar Zamfara da kuma razana wadanda suke shirin aikata aiki irin haka.” a cewar sanarwar.

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...