Gwamnatin tarayya za ta kashe  biliyan 12 wajen daga darajar wasu asibitoci

Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince a kashe  naira biliyan 12 domin a sayen wasu muhimman kayayyakin kiwon lafiya a wasu asibiti dake jihohi 6  na Najeriya.

Da yake magana bayan taron majalisar da shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta a ranar Talata ministan lafiya, Dr Muhammad Ali Pate ya ce za a inganta kayayyakin aikin ne asibitocin domin fadada damar samun kiwon lafiya.

Pate ya ce za ayi amfani da kuɗin wajen sayen manyan kayayyakin gwaje-gwaje da suka haɗa da  na’urar MRI ta ɗaukar hoton ƙwakwaf da kuma na’urar yin Scan guda biyu.

Asibitocin da za su amafana da shirin sun haɗa da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Uyo a jihar Akwa Ibom, Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Abeokuta, Jami’ar Obafemi Awolowo a jihar Osun Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Keffi a jihar Nasarawa, Asibitin Koyarwa na Moddibo Adama dake Yola da kuma Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya dake Kebbi.

More from this stream

Recomended