Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a ya ce gwamnatin tarayya na shirin buɗe rumbunan adana kayan abinci domin rage tsadar kayan abinci.
A ranar Litinin ne wasu mazauna garin Minna babban birnin jihar Niger suka rufe wasu titunan birnin a yayin da suke gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake fama da ita.
Har ila yau a birnin Kano an gudanar da makamanciyar irin wannan zanga-zanga.
A ranar Talata kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa don gaggauta samar da abinci ya gudanar da wani taron gaggawa a fadar Aso Rock.
Da yake magana da yan jaridu a ranar Laraba, Idris ya ce gwamnati ta damu sosai da halin da ƴan Najeriya suke ciki.
Ya ce taron da suka gudanar ba shi ne na ƙarshe ba za a cigaba da gudanar da makamancinsa.