Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allawadai Da Harin Da Ya Lalata Turakun Wutar Lantarki A Yobe

Gwamnatin tarayya tayi allawadai da harin da aka kai kan manyan turakun lantarki dake kai wuta jihar Yobe.

A wani sako da ya wallafa a shafin X ranar Asabar, ministan harkokin wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya ce ya kadu matuka kan barnar da aka aikata da gangan.

A ranar Alhamis ne alummomin wasu daga cikin garuruwan dake jihar Borno da Yobe suka fada cikin duhu biyo bayan harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan manyan turakun lantarki dake kai wuta jihohin biyu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma’a kamfanin dakon wutar lantarki na TCN ya ce an lalata daya daga cikin turakunsa T372 dake wajejen kauyen Katsaita a jihar Yobe.

Harin na baya bayan nan na zuwa ne shekara biyu bayan da yan ta’addar suka lalata turakun wutar da ya jefa baki dayan jihar cikin duhu.

Adelabu ya ce da gangan ya ta’addar suka saka abubuwan fashewa a turakun wutar lantarkin dake daukar wuta mai karfin 330KVA.

Ministan ya ce mazauna kauyen sun ji kara gabanin faduwar turken wutar.

More from this stream

Recomended