Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen kashe-kashen da ke addabar wasu al’ummomi a jihar Filato, musamman a kananan hukumomin Bokkos da Bassa.
Badaru ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da ya kai ziyarar jaje ga al’ummomin da aka kai wa hari a karamar hukumar Bassa, inda fiye da mutane 100 suka rasa rayukansu, kana dukiyoyi da dama suka salwanta cikin makonni uku da suka wuce.
“Mun zo a madadin gwamnatin tarayya domin nuna alhini da kuma jajantawa dangin wadanda suka rasa rayukansu. Gwamnati na bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji Badaru.
Ya kara da cewa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya damu matuka da abin da ke faruwa a nan, kuma ya umarce mu da mu zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci hukunci.”
Ministan ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnati na aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar Filato don samar da tsari mai dorewa da zai hana faruwar irin wannan lamari nan gaba.
A nasa bangaren, Sarkin Irigwe, Brra Ngwe Ronku Aku, ya gode wa ministan bisa wannan ziyara, tare da rokon gwamnati da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen kawo karshen hare-haren da ke ci gaba da jefa mutanen yankin cikin fargaba da asarar rayuka da dukiyoyi.
Sarkin ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta taimaka wajen sake gina gidajen da aka kona, da kuma samar da kayan more rayuwa ga wadanda lamarin ya shafa domin su farfado da rayuwarsu.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Kisan Jama’a a Jihar Filato
