Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar hutun bikin samun ƴancin kai

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun bikin tunawa da ranar da Najeriya ta samu ƴan cin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya..

Olabunmi Tunji-Ojo ministan harkokin cikin gida shi ya sanar da hotun a ranar Asabar a wata sanarwa da babbar sakatariyar dindin ta ma’aikatar, Magdalene  Ajani to ta fitar.

Ministan ya yabawa ƴan Najeriya dake da haƙuri da aiki tuƙuru inda ya ƙara da cewa sadaukarwa da suka nuna baza ta tafi haka kawai ba.

Ya kuma jaddada buƙatar ƴan Najeriya da suyi duba kan sadaukarwar da gwarazan da suka kafa ƙasar.

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa baza ayi bikin shagulgula sosai ba na tunawa da ranar saboda halin matsin rayuwa da al’umma suke fuskanta.

More News

Sojoji sun kama ƴan bindiga biyu da suka je asibiti a duba lafiyar su

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu ƴan bindiga biyu dai-dai lokacin da suka je asibiti domin a duba lafiyar su a...

Sojoji sun kama ƴan bindiga biyu da suka je asibiti a duba lafiyar su

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu ƴan bindiga biyu dai-dai lokacin da suka je asibiti domin a duba lafiyar su a...

Jami’an EFCC sun kai samame gidajen kwanan ɗaliban UDUS

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kai wani samame da tsakar dare a kan gidajen kwanan dalibai na...

Wasu matasa uku da ake zargi da garkuwa da mutum sun gurfana a gaban kotu a Kano

Wasu matasa guda uku sun bayyana a gaban wata kotun majistire dake zamanta a unguwar Gyadi-Gyadi dake Kano inda ake tuhumarsu da zargin  yin...