Gwamnatin Tarayya ta sake gayyatar ƴan ƙwadago kan ƙarin albashi

Gwamnatin tarayya ta sake mika goron gayyata zuwa ga kungiyar kwadago domin ci gaba da tattaunawa kan batun mafi karancin albashi, kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Majiyar ta bayyana cewa Labour za ta mutunta wannan gayyata.

“Shugaban kwamitin ya aike da wasika zuwa ga kungiyar kwadago kuma shugaban NSIWC ya sanya mata hannu. An shirya taron ne a ranar Juma’a.

“Tabbas, Labour za ta halarta. Idan sun gabatar da abu mafi kyawu a ranar Juma’a za mu karba.”

A ranar Talata ne kwamitin mafi karancin albashi ya dage zamansa bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar Kwadago ta wargaje yayin da ma’aikata suka ki amincewa da sabon kudirin gwamnatin tarayya na Naira 60,000, sama da yadda aka saba a baya na tayin N57,000.

More from this stream

Recomended