Gwamnatin tarayya ta janye hanin haƙar ma’adinai a jihar Zamfara

Gwamnatin tarayya ta janye hanin da tayi na haƙar ma’adinai a jihar Zamfara wanda ta saka a shekarun baya.

A shekarar 2019 ne gwamnatin tarayya ta hana duk wasu ayyukan haƙar ma’adinai a jihar ta Zamfara inda ta umarci ƴan kasashen waje dake da wuraren haƙar ma’adanai da su fice daga jihar.

Har ila yau gwamnatin ta ƙaddamar da wani shiri na musamman na yaƙi da ƴan fashin daji dake ɗauke da makamai.

Da yake magana a wurin wani taron manema labari da aka ayi, Dele Alake  ministan haƙar ma’adinai ya ce an ɗauki matakin ne saboda yanayin ingatuwar tsaro da aka samu a jihar.

Har ila yau wata anarwar da aka fitar ranar Lahadi mai taimakawa ministan ya ce Najeriya za ta anfana sosai matuƙar aka dawo da aikin haƙar ma’adinai.

More from this stream

Recomended