Gwamnatin tarayya ta cire haraji kan kayan abinci da aka shigo da su

Gwamnatin tarayya ta dakatar da kuɗin fito, haraji akan kayan abinci da aka shigo da su.

A wata sanarwa ranar Litinin, Abubakar Kyari  ministan harkokin noma da wadata ƙasa da abinci ya ce an cire harajin shigo da kaya, kuɗin fito da kuma haraji akan kayan abinci irinsu shinkafa sanfarera,alkama, masara, da kuma wake da aka shigo da su ta ruwa ko kuma ta ƙasa.

Kyari ya ce za a ɗauki tsawon kwanaki 150 domin tabbatar an aiwatar da matakin tsarin na cire harajojin da za a aiwatar da shi a cikin kwanaki 180 masu zuwa domin rage hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Ya ce mataimakin na daga cikin tsarin dai-daita farashi da kwamitin kula da tattalin arzikin ƙasa ya  gabatarwa da shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ya ƙara da cewa kowa sheda ne kan yadda kayayyakin abinci suka yi tsada sosai cikin ƴan watanni kuma matakin da aka ɗauka na nuni da cewa ana sane kuma gwamnati na sauraron koken ƴan Najeriya.

More from this stream

Recomended