Gwamnatin tarayya ta ci alwashin hukunta yan bindigar da suka kashe masallata a Katsina

Muhammad Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar an kama tare da hukuncin a waɗanda suka kai hari kan masallata a ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Ranar Talata ne wasu yan bindiga suka kai hari kan wasu mutane dake sallar Asuba a wani masallaci inda su ka kashe masallata da kawo yanzu yawansu ke cigaba da karuwa.

A ranar Laraba, sakataren gwamnatin jihar Katsina ya tabbatar da mutuwar mutane 32 a harin.

A cikin wata sanarwa ranar Juma’a ministan ya bayyana kisan da cewa “tsantsar rashin imani ne da dabbanci” inda ya kara da cewa harin ta’addanci irin wannan baza a kyale shi ya samu gindin zama ba a kasar nan.

Ministan ya ce tuni jami’an tsaro suka fara bibiyar sawun maharan inda ya bada tabbacin cewa gwamnati baza ta yi kasa a gwiwa ba ya sai an kama su tare gurfanar da su gaban Shari’a.

More from this stream

Recomended