Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 5 ga watan Satumba, 2025, a matsayin ranar hutu don gudanar da bikin Maulidin Annabi Muhammadu (SAW).
Wannan sanarwar ta fito ne daga ofishin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, inda sakatariyar dindindin ta ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta sanya hannu a kai a ranar Talata a Abuja.
A cikin sanarwar, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya aika sakon taya murna ga al’ummar Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un Annabi Muhammadu (SAW) na zaman lafiya, soyayya, kaskantar da kai, hakuri da tausayi. Ya ce wadannan dabi’u ne ginshiƙan da za su iya tabbatar da ƙasa ɗaya mai ci gaba.
