Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Aikin Layin Dogo a Kano a Naira Tiriliyan Ɗaya

Gwamnatin Tarayya ta amince da gina Layin Dogon Kasa na Birnin Kano da zai lakume kudi Naira tiriliyan daya, wani babban aiki da ake sa ran zai sauya harkar sufuri a birnin tare da bunkasa tattalin arzikin jihar.

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga ‘yan tawagar Kano da suka halarci Gasar Karatun Alkur’ani ta Kasa ta shekarar 2025 da aka gudanar a Jihar Borno.

Sanarwar ta fito ne a wata takarda da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

A cewar gwamnan, aikin layin dogon kasar an tsara shi ne domin samar da ingantaccen tsarin sufuri na zamani mai saukin kudi, wanda zai hada muhimman yankuna a cikin birnin Kano, rage cunkoson ababen hawa, da saukaka zirga-zirgar al’umma.

Gwamna Yusuf ya ce aikin na nuna sabon tsarin siyasar gwamnatinsa da Gwamnatin Tarayya karkashin jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan an yi shi ne domin jawo muhimman ayyukan ci gaba zuwa Kano.

More from this stream

Recomended