Gwamnatin tarayya ta amince a riƙa sayarwa matatar man Dangote ɗanyen  mai a farashin naira

Majalisar Zartarwa ta tarayya ta amince da bukatar da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar mata dake umartar kamfanin mai na Najeriya NNPCL da ya riƙa sayar da ɗanyen mai ga matatar Dangote da sauran matatun mai akan kuɗin naira.

A wata sanarwa a kafar sadarwa ta X da akafi sani da Twitter a baya mai bawa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce bankin shiga da fitar da kayayyaki na Afrika wato Afriexim Bank da kuma wasu bankuna su ne za su ƙulla cinikin tsakanin Dangote da NNPCL.

Majalisar zartarwar ta amince da buƙatar ne a yayin zamanta na ranar Litinin da shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta.

A ƴan kwanakin nan ana ta taƙaddama akan batun matatar man ta Dangote inda wasu ke zargin cewa ana yiwa matatar zagon ƙasa.

Amincewa da matakin na nufin kamfanin mai na NNPCL zai riƙa sanarwar da matatar ta Dangote gangar mai 450,000 a kowace rana da ake warewa matatun gida.

More from this stream

Recomended