Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Gwajin Ƙwaya Ga Masu Neman Aikin Gwamnati

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana shirin fara gwajin ta’ammali da ƙwayoyi ga duk masu neman aikin gwamnati a ƙasar, inda ta ce daga yanzu gwajin zai zama wajibi kafin a ɗauki kowane mutum aiki.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya fitar a madadin gwamnati.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnati za ta haɗa hannu da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) domin tabbatar da nasarar aiwatar da shirin.

Gwamnati ta ce ɗaukar wannan mataki ya zama dole sakamakon ƙaruwa da yawaitar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasan Najeriya.

More from this stream

Recomended