Gwamnatin Tarayya ta ƙara kuɗaɗen makarantun sakandarenta zuwa N100,000

Kwalejojin Gwamnatin Tarayya (FGCs), wanda aka fi sani da Federal Unity Colleges, yanzu suna karbar kudin karatu fiye da da, wanda daga 45,000 ya tashi zuwa 100,000.

An bayyana hakan ne a cikin wani umarni da aka aika zuwa ga dukkan shugabannin Kwalejin Unity ta Tarayya a ranar 25 ga Mayu, 2023, mai lamba ADF/120/DSSE/I, daga ofishin daraktan Sashen Ilimi na Babbar Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

Takardar da Daraktar manyan makarantun gaba da sakandire Hajiya Binta Abdulkadir ta sanya wa hannu ta bayyana cewa ana sa ran sabbin dalibai za su fara biyan ₦100,000 maimakon ₦45,000.

Hakan dai na zuwa ne duk da cewa majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya a ranar 11 ga watan Yuli da ta daina kara kudin karatu a dukkan makarantun sakandare mallakar gwamnatin tarayya.

More from this stream

Recomended