Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin bikin ranar dimakwaradiya.
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya ayyana haka a madadin gwamnatin tarayya a ranar Talata cikin wata sanarwa da Dr Aishatu Gogu Ndeyako babbar sakatariya a ma’aikatar cikin gida ta fitar.
Tunji-Ojo ya yadda cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu na cigaba da mayar da hankali wajen kawo kyawawan sauye-sauye da za su farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
” A yayin da muke bikin ranar dimakwaradiya a tarihin ƙasar mu.Ya kamata muyi duba kan ƙoƙarin da waɗanda suka samar da ƙasar suka yi ta hanyar tabbatar da Najeriya ta cigaba da zama dunƙulalliyar ƙasa mai cike da tsaro da zaman lafiya,” ya ce.
Ya kuma ya yi kira gan ƴan Najeriya dama kawayen Najeriya da suyi duba su yaba cigaban da aka samu.