Gwamnatin Sokoto za ta tura ƴan jiharta karatu China

Gwamnatin jihar Sokoto ta dauki nauyin dalibai 15 ‘yan asalin jihar domin yin karatu a kasar Sin.

Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Sokoto, Abdulkadir Dan’iya ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ofishinsa ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa daliban za su karanci kwasa-kwasan injiniyanci.

A cewarsa, za su bar kasar ne a mako na farko ko na biyu na watan Nuwamba.

“A halin yanzu suna fuskantar wani nau’i na daidaito wanda ya zama dole don zama a wata ƙasa. Gwamnatin jihar ta riga ta fitar da kudade don karatunsu da kuma kula da su,” in ji shi

More from this stream

Recomended