Gwamnatin Sokoto ta bayar da tallafin miliyan 20 ga mutanen ƙauyen da aka da jirgin yaƙi ya sakarwa bam

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ziyarci ƙauyen da jirgin saman sojan Najeriya ya sakarawa inda ya duba girman barnar da harin ya jawo tare da jajantawa da kuma ta’aziyar mutanen da suka rasu

A cewar Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta ƙasa NEMA a cikin wani saƙo da ta wallafa a X a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce sama da mutane 10 aka tabbatar sun mutu a bam ɗin da aka saka kan ƙauyuka biyu dake ƙaramar hukumar Silame ta jihar..

Jirgin saman yaƙin ya yi yunkurin sakar da bam ɗin ne kan mayaƙan Lakurawa amma aka samu kuskure ya sake shi akan ƙauyukan Gidan Bisa da Rintawa.

Gwamnan jihar ta Sokoto ya ce ya yi baƙin ciki matuƙa da samun labarin kai harin a matsayin sa na gwamnan jihar.

A lokacin ziyarar da ya kai garuruwan da abun ya faru ya bayar da tallafin kuɗi naira miliyan 20 tare da buhuna 100 na kayan abinci.

More from this stream

Recomended