Gwamnatin jihar Plataeu ta saka dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta arewa da kuma Jos ta kudu biyo bayan harin da ya faru wanda ya jawo asarar rayuka tsakanin daren Alhamis ya zuwa wayewar garin ranar Juma’a.
Jaridar The Cable ta gano cewa mutane 14 ne suka rasa rayukansu a rikicin.
Wasu yan bindiga ne suka kai harin wani gida dake yankin titin Rukuba a karamar hukumar Jos ta arewa inda suka kashe wasu iyalai su 7.
Lamarin ya jawo zanga-zanga daga wasu mata da suka hasala.Matan sun kona wata motar soja da ta kai sojoji wurin da lamarin ya faru abin da ya jawo sojojin suka bude wuta.
Wasu matasa sun bazama kan tituna da safiyar ranar Juma’a domin yin zanga-zangar abinda suka kira “rashin zuwan sojoji akan lokaci.”
Richard Tokma, mai rikon muƙamin sakataren gwamnatin jihar shine ya sanar da sanya dokar hana fitar a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce dokar hana fitar zata fara aiki ba tare da wani jinkiri ba tun daga karfe biyar na yamma zuwa shida na safe.
Terna Tyopev, mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai bayar da adadin mutanen su suka mutu ba.