Gwamnatin Neja za ta rika bayar ga lada ga masu tsegunta mata bayanai

Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da ba yarda lada ga duk wadanda za su rika tsegunta mata bayanai sirri kan bata gari da suka matsawa jihar.

Babbar jami’ar watsa labarai ta gwamnan, mary Noel-berje ta shaida wa jaridar Daily Trusta ranar Asabar cewa an dauki matakin ne sakamakon karuwar hare-hare da ake samu a ‘yan makwannin nan.

“Gwamna Sani Bello ya samar da wani daki turawa da kuma bayanan sirri ga jami’an tsaro domin kai dauki cikin gaggawa,” in ji ta.

An tambayeta nawa ne ladan da za a rika bayarwa, sai ta ce ba wannan ba ne mafi mahimmanci zaman lafiyar mutane shi ne mafi a’ala.

More from this stream

Recomended