Gwamnatin Najeriya ta nuna rashin gamsuwarta game da tsadar siminti

Gwamnatin tarayya ta ce kamfanonin da ke samar da siminti ba sa yin abin da ya dace wajen dakile hauhawar farashin siminti a kasar.

Gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta amince da yanayin da farashin kayan gini kamar siminti ke ci gaba da tashi ba tare da kayyadewa ba.

Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc.  Ahmed Dangiwa, ya bayyana haka a lokacin da ya gayyaci masu sana’ar siminti zuwa wani taro a hedkwatar ma’aikatar da ke Abuja, a ranar Talata 20 ga Fabrairu, 2024.

Arc.  Dangiwa ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda farashin siminti da sauran kayayyakin gini ke ci gaba da tabarbarewa, sannan ya zargi kamfanonin da ke fakewa da canjin kudi da cewa su ke wahalar da ‘yan Najeriya.

More News

Tinibu ya aikawa da majalisar dattawa sunaye 7 na  ministocin da zai naÉ—a

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga majalisar dattawa da ta tabbatar da sunayen mutane 7 da ya tura majalisar da zai...

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...