Gwamnatin Najeriya ta kara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC ‘alawee’ zuwa N77,000

Gwamnatin tarayya ta kara yawan alawus din masu yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa N77,000 duk wata, daga Yuli 2024.
 
Wannan ci gaban ya biyo bayan kafa dokar mafi karancin albashi na kasa 2024, kamar yadda wata sanarwa da mukaddashin daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta NYSC Caroline Embu ta fitar.
 
Hukumar kula da albashi ta kudaden shiga ta kasa ta tabbatar da karin alawus din a wata wasika mai dauke da kwanan wata 25 ga Satumba, 2024, mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatar Ekpo Nta.
 
Darakta Janar na NYSC Birgediya Janar Y.D. Ahmed a baya ya bayar da shawarar inganta jindadi ga mambobin na NYSC.

Ya kuma nuna godiya ga Gwamnatin Tarayya.
 
An ambato shi yana cewa, “Ina godiya da wannan karamcin da aka yi a kan lokaci, wanda zai kawo taimako ga ‘yan bautar ƙasa, da kara musu kwarin gwiwa, da zaburar da su wajen yi wa kasa hidima.
 
Sabon alawus din dai ya nuna karin kashi 133 cikin 100 daga kudaden alawus din da ake biya na Naira 33,000 a baya.

More from this stream

Recomended