HomeMoreGwamnatin Najeriya Ta Bada Umurnin Dakatar Da Daukar Aiki | BBC Hausa

Gwamnatin Najeriya Ta Bada Umurnin Dakatar Da Daukar Aiki | BBC Hausa

Published on

spot_img

Wannan umurni na dakatar da daukar ma’aikata ya shafi dukkan ma’aikatun gwamnati, har ma da maye gurban ma’aikatan da suka yi ritaya. Matakin na zuwa ne bayan karyewar kudin danyen Mai a kasuwar duniya wanda har ya sa gwamnatin kasar ta rage yawan kasafin kudinta na bana.

To sai dai wannan matakin bai yi wa kungiyar kwadago ta ULC dadi ba, domin shugaban tsare-tsaren kungiyar kwamared Nasiru Kabir ya ce ba zasu yi shiru ba, zasu yi wa fadar shugaban kasa wasika ta musamman domin ta janye wannan mataki, ganin cewa har yanzu miliyoyin matasa na yawo da takardun kammala karatu amma babu ayyukan yi. Kungiyar kwadagon ta kuma yi barazanar yin kiran yajin aiki na gama gari idan gwamnati bata sauya matakin ba, a cewar kwamared Nasiru.

Shi kuma tsohon mukaddashi shugaban kungiyar ma’aikatan Mai ta kasa, Komred Isa Tijjani, ya ce wannan rufa-rufa ne gwamnati ke yi, ya kamata ta fito ta gaya wa ‘yan kasa gaskiyar cewa ba ta da kudi a lalitar ta, a saboda haka dukkan alkawulan da ta yi ba za ta iya aiwatar da su ba.

Isa Tijjani ya kuma ce wannan yanayi ba zai yi wa kasar kyau ba domin mutane sun kai makura a halin ha’ula’in’ da suka tsinci kansu a ciki tsawon shekara biyar.

Amma kwararre a kimiyar tattalin arziki na kasa-da-kasa, Yusha’u Aliyu, ya ce wanan karyewar tattalin arzikin ya shafi duniya ne baki daya, saboda haka duk gwamnatin da ta san abinda ta ke yi, za ta dauki matakan kawo sauki.

A halin yanzu dai gwamnati ta ce matakin saukin da ta dauka shi ne na rage kudin man fetur daga Naira 145 zuwa Naira 125.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this