Gwamnatin Lagos ta fara kama masu kwashe shara da basu da mota

Jami’an hukumar kwashe shara ta jihar Lagos sun kama wasu masu kwashe shara da basu da rijista inda aka ƙwace kurar aikinsu.

Hukumar ta gudanar da kamen ne ga yankin Abule-Egba, Oshodi, Agege, Dopemu da kuma wasu sassan jihar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin X a ranar Asabar, Muyiwa Gbadegesin shugaban hukumar ya ce masu kwashe shara a kura suna sanya birnin ya zama bashi da kyan gani.

Ya ce tawagar jami’an hukumar dake yaƙi da masu kwashe shara a kura a ƙarƙashin Idowu Sanni su ne suka yi aikin kamen.

More from this stream

Recomended