Gwamnatin jihar Katsina ta shirya tsaf domin fara aiwatar da wani tsari na sayar da kayan amfanin yau da kullum akan farashi mai rahusa.
Sabon shirin zai ƙunshi samar da shaguna 38 da aka yiwa laƙabi da ‘Rumbun Sauki’ a fadin ƙananan hukumomin jihar 34.
Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda shi ne ya sanar da shirin samar da kantunan a ƙananan hukumomin jihar bayan amincewar da majalisar zartarwar jihar ta yi a taron ta na 10.
Engr Yakubu Muhammad Danja mai bawa gwamnan jihar shawara kan bunƙasa tattalin arzikin karkara ya ce dukkanin wasu shirye-shirye sun kammala domin fara aiwatar da shirin.
Ya ce birnin Katsina zai samu ƙarin kantuna 2 a yayin da ƙananan hukumomin Funtua da Daura za su samu karin kanti ɗaya -ɗaya.
Ya ƙara da cewa ana sa ran nan gaba za a faɗada shirin ta hanyar samar da kantunan a dukkanin mazaɓun jihar 361.