Hukumar da’ar ma’aikata ta jihar Kano ta amince da karin girma ga manya da kananan ma’aikata 118 a ma’aikatu da sassa da hukumomi 13.
Shugaban hukumar Dr Umar Shehu Minjibir ne ya bayyana hakan bayan zaman hukumar a Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na hukumar Musa Garba ya fitar jiya.
Dokta Minjibir ya ci gaba da cewa adadin wadanda aka yi wa karin girma tun bayan kaddamar da hukumar da ya jagoranta a watan Agustan wannan shekara sun kai 379.
A yayin da yake yabawa da jajircewar ma’aikatan a fadin hukumar, shugaban ya yi kira ga ma’aikatan da aka kara musu girma da su maida hankali wajen yin aiki tukuru domin samun sakamako mai kyau.