Gwamnatin Kano ta ci alwashin karɓo yaran da suka fito da jihar daga cikin waɗanda aka gurfanar a gaban kotu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin karɓo yaran da suka fito daga jihar daga  cikin waɗanda ake tsare da su a Abuja.

Yara da dama ne dai aka gurfanar da su a gaban kotu a ranar Juma’a kan zargin da ake musu na shiga cikin zanga-zangar #Endbadgovernance da aka yi a cikin watan Oktoba.

An ce waɗanda aka kama ɗin sun fito ne daga jihohin Kaduna, Kano, Katsina,Gombe, Filato da kuma birnin tarayya Abuja.

Bayan gurfanar da su ɗin ne kotu ta bayar da belinsu kan kuɗi naira miliyan 10 kowannensu.

Ƴan Najeriya da dama da suka haɗa da ƴan siyasa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu sun yi allawadai da yadda aka jefa yaran cikin mawuyacin hali na yunwa a tsawon lokacin da suka shafe a tsare.

Da yake mayar da martani kan batun gwamnan ya ce tuni aka umarci kwamshinan Shari’a na jihar, Haruna Isa Dederi da ya ɗauki mataki kan lamarin.

“Za muyi duk mai yiyuwa domin dawo da su Kano, Insha Allah,” a cewar gwamnan cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X.

More from this stream

Recomended