Gwamnatin Kaduna ta ceto yara 13 da aka sayar da su a jihar Enugu

Gwamnatin jihar Kaduna ta ceto wasu yara 13 da ake zargin an sayar da su ga masu safarar mutane a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Kwamishiniyar ma’aikatar gina al’umma da samar da cigaba ta jihar Hajiya Rabi Salisu ce ta sanar da haka lokacin da take magana da manema labarai.

Ta ce tunda farko wasu mutane da kawo yanzu ba a kama wasu daga cikinsu ba ne  suka fara ajiye yaran a Abuja kafin daga bisani su wuce da su jihar Enugu.

“Ɗaya daga cikin yaran da aka sace shi yana da kwana 7 da haihuwa amma yanzu yaran yana da shekaru 7. Yaran baza su iya gane inda suka fito ba amma hukumomi za suyi duk mai yiyuwa wajen tabbatar da ganin an haɗa dukkanin yaran da iyayensu,” ta ce.

Ta ƙara da cewa dukkanin yaran an canza musu suna daga na

Hausa ya zuwa wani sunan na daban .

More from this stream

Recomended