Gwamnatin jihar Sokoto za ta sayawa marayu shanun miliyan ₦14.68

[ad_1]








Gwamnatin jihar Sokoto ta raba kuɗi naira miliyan ₦14.68 domin sayan shanun sallah ga marayun dake gundumomi 88 dake jihar.

A cewar shugaban hukumar Zakka ta jihar, Mallam Lawal Maidoki ya ce an ɗauki matakin ne domin suma su yi bikin sallah cikin walwala kamar sauran yara.

Ya ce kowace gunduma zata karbi kuɗin da ba su gaza ₦160000 domin su sayi saniya su yanka kana su raba naman ga marayun dake gundumar.

Anasa jawabin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yabawa hakimai kan sadaukarwar da suka nuna wajen tabbatar da shirin ya samu na nasara a yankunansu.




[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...