Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da fara biyan mafi ƙarancin albashi na naira 70,000 ga ma’aikatan jihar daga gobe Litinin.
Sanarwar ta fito ne daga gwamnan jihar, Ahmad Aliyu, wanda ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook. Ya ce sabon tsarin biyan albashin zai shafi ma’aikatan gwamnatin jiha da na ƙananan hukumomi.
Gwamnan ya kuma yi kira ga ma’aikatan jihar da su mayar wa gwamnati ta hanyar yin aiki da ƙwazo da kuma cika aikinsu yadda ya kamata.
Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Kaddamar Da Mafi Ƙanƙantar Albashi Na Naira 70,000
