Gwamnatin jihar Niger ta fara rabon kayan tallafi

Gwamnatin jihar Niger ta fara raba tallafin shinkafa mai saukin farashi ga mazauna jihar.

Da yake magana da yan jarida a Minna ranar Asabar, Mustapha Jibrin shugaban kwamitin rabon tallafin a mazabar Tudun Wada south ya ce tallafin kayan da kudinsu ya kai miliyan 20 aka raba a mazabar.

Jibrin wanda ya samu wakilcin Sirajo Sama’ila ya ce mazabar ta kunshi akwatun zabe 50 kuma ita ce mafi girma a karamar hukumar Chanchanga ta jihar.

“mazabar ita tafi yawan tashoshin zabe, mun yarda cewa gidaje 70 daga kowace akwatun zabe za su amfana” ya ce.

Ya ce an yi haka ne saboda tallafin ba zai ishi a bawa kowa ba duk da cewa mai yawa aka saya.

Shugaban ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya da kuma ta jiha kan amincewa da rabon tallafin domin rage raÉ—aÉ—in cire tallafin cire man fetur.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...