
Asalin hoton, S T YAKASAI
Gwamnatin jihar Kano ta musanta rufe asibitin, amma ba ta yi karin haske kan ko ta na da masaniya game da umarnin da kotu ta bada na rufe asibitin
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rufe ayyukan asibitin yara da ke titin Gidan Zoo a cikin birnin Kano bayan shafe kusan shekaru uku da fara aiki.
Matakin gwamnatin na Kano ya dai kawo tsaiko wajen harkokin duba marasa lafiya, sakamakon yadda ma’aikatan asibitin suka gaza sanin makomarsu yayin da marasa lafiya ke kokawa.
Abokin aikinmu a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, wanda ya ziyarci asibitin yara na Isyaka Rabi’u da ke hanyar gidan adana namun daji, ya ce a sabanin yadda asibitin ke cika makil da marasa lafiya da koke-koken yara, a yanzu shiru kake ji.
Wasu daga cikin marasa lafiya da ke jiyya da kuma ba a sallame su daga asibitin ba, sun yi tagumi suna tunanin a makomar rayuwa, sakamakon fargabar halin da za su shiga idan likitoci da malaman jinya suka daina zuwa aiki.
A cewar daya daga cikin jagororin asibitin da ya nemi a sakaya sunan sa, suna tsaka da yin aiki ne sai suka sami wani umarnin kotu cewar kamfanin da ke kula da ayyukan wannan asibiti mai suna Northfield Health Services ya ba da umarnin kwashe kayansu daga asisbitin tare da ma’aikatan sa baki daya.
“Ba mu san makomar mu ba, saboda babu wani bayani da akai mana, wadanda ke kula da asibiti da shugabannin asibitin ne suka samu sabani, don haka sai an warware matsalar,” in ji shi.
Sai dai shugaban hukumar da ke kula da asibitoci a Kano, Dr Nasiru Kabo, ya shaida wa BBC cewar gwamatin Kano ba ta rufe asibitin ba, amma ta janye yarjejeniyar kawance aiki tsakanin ta da kamfanin Northfield Health Services saboda rashin gamsuwa da yadda yake kula da asibitin.
Bai dai yi karin bayani dangane da inda aka sami umarnin kotun ba tare da yin cikakken bayani kan makomar asibitin.