Gwamnatin jihar Borno Ta Kashe Sama Da Naira Miliyan 500 Don Sayen Kayan Gyaran Wasu Hanyoyi

[ad_1]

Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta soma aikin shimfida hanya daga garin Gamboru Ngala zuwa karamar hukumar Kala Balge domin baiwa al’ummar yankin damar gudanar da harkokinsu cikin sauki.

Gwamnan jihar Kashim Shettima ne ya bayyana hakan, yayinda yake kaddamar da wasu taraktoci da aka sayo akan kudi fiye da Naira milyan 550m domin soma aikin shimfida hanyar da ta tashi daga garin Gamboru zuwa Kala Balge da suke makwaftaka da kasar Kamaru. Yankin dai yayi fama da hare-haren ‘yan Boko Haram a can baya.

Hanyar Kala Balge na da tazarar kilomita 35 daga Gamboru Ngala, amma tun kafa karamar hukumar fiye da shekaru 30, ba’a taba shimfida hanayr kwalta zuwa garin ba. Abunda yake faruwa shine da zarar damina ta fadi mutanen dake Ran cikin karamar hukumar Kala Balgen, kan kaura zuwa wasu garuruwan cikin wasu kananan hukumonin d suke kusa,saboda munin hanyar da kan hana motoci shiga yankin.

Kazalika gwamnatin ta ce za’a soma aikin hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngalan.Yanzu dai hanyar ta na cikin mummunan yanayi. Hanyar ita ce ta tashi daga Maiduguri zuwa wasu kasashen Afirka da ‘yan kasuwa da yawa ke binta.

A hira da Sashen Hausa na Muriyar Amurka kwamishinan ma’aiatar ayyuka na jihar Alhaji Adamu Lawan,yace hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala, hanya ce ta gwamnatin tarayya wadda gwamnatin tarayyar ta baiwa wani kamfanin kasar China. Amma sabida ‘yan Boko Haram suna kakkashe ‘yan kasar da suke aiki da kamfanin, sai suka bar aikin. Kwamishina Lawal yace saboda haka ne suka je ma’aikatar ayyuka ta tarayya suka yi yarjejeniya domin su ci gaba da aikin.

A cewar kwamishanan sabuwar hanyar daga Gamboru Ngala zuwa Kala Balge mai tazarar kilomita 35 ba za ta dauke su watanni biyar zuwa shida ba da zasu gama.

A saurari rahoton Haruna Dauda

[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...