Gwamnatin Jigawa ta raba wa ƴan sanda baburan sintiri 30

Gwamna Malam Umar A Namadi, ya baiwa rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar Jigawa tallafin babura 30 na sintiri.

Da yake jawabi a lokacin da yake gabatar da baburan, Gwamna Namadi ya ce baburan za su inganta sa ido da kuma daukar matakan dakile masu aikata laifuka a jihar.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa tallafin shi ne kashi na farko na rabon babura/motoci ga hukumomin tsaro da gwamnati mai ci ke yi.

“Wannan shi ne kashi na farko na rabon ababen hawa ga jami’an tsaro da gwamnatin yanzu ta raba. Yayin da ‘yan sandan Najeriya za su ci gajiyar tallafin na yau, sauran hukumomin tsaro ma za su samu irin waɗannan tallafin a zango na gaba,” inji shi.

More from this stream

Recomended