Gwamnatin Filato Ta Ce Yawan Makamai A Hannun Jama’a Ke Haddasa Rikici

Hukumar dake wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta bayyana takaicinta akan yawatar makamai a jihar dake hannun jama’a lamarin da ta alakanta ta ruruwa wutar rikici a jihar.

Cikin ‘yan kwanakin nan da rikici ya barke a babban birnin jihar, bayanai sun nuna cewa mutane da dama sun mallaki makamai ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya haddasa kashe mutane da dama tare da kone dukiyoyi a cikin birnin.

Shugaban hukumar wanzar da zaman lafiya da sasanta al’umma a jihar Joseph Lenmak, ya ce gwamnati da hukumomin tsaro za su dukufa wajen tabbatar da jama’a sun mika makaman dake hannunsu ga hukuma.

A cewarsa abun da ya faru yakamata kowa ya nuna bacin rai akai.Kamar akwai wasu mutane da ba sa son zaman lafiya a jihar.

Dangane da yawan makamai, Joseph Lenmak ya ce ba abu mai kyau ba ne a ce an tara makamai a gidaje. Irin wannan abun ba zai haifar da zaman lafiya ba. Idan aka ci gaba haka ko yau ko gobe ana iya fadawa cikin wani babban bala’i.

Mr Lenmak Ya ce irin makaman da aka fito dasu ana yaki abun ya wuce gona da iri. A cewarsa gwamnati za ta yi iyakacin kokarinta ta shawo kan lamarin. Ya ambaci kananan hukumuomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Barkin Ladi a matsayin wuraren da aka fi mallakar makamai. Ya ce dole ne a hada kai a zauna tare domin babu wanda zai ci nasara shi kadai.

Baya ga yawaitar makamai, yayata labarun karya ma na kara ruruta wutar rikici a jihar a cewar Lenmak. Ya kira gidajen rediyo, da kafofin sadarwa na zamani da jaridu da mutane da babbar murya cewa su daina yada labarun karya. Su binciki kowane irin labari suka samu su tabbatar na gaskiya ne domin idan garin ya kama wuta kowa zai shafa.

More News

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...