Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin ajiye gawarwaki dake jihar.
Gwamnatin ta ce anyi yunkurin karbar harajin ne bawai dan saboda gwamnati tana son tara kuɗi ba.
Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta jihar Enugu, Emmanuel Nnamani lokacin da yake mayar da martani kan takardar harajin da aka aikawa gidajen ajiye gawa dake jihar wacce ake ta ce-ce-kuce akai a kafafen sadarwar zamani.
A cewarsa harajin na cikin ƙudirin dokar Harajin Gidajen Ajiye Gawa dake jihar da ta daɗe ana amfani da ita kuma ba sabon abu ba ne a jihar.
Nnamani ya bayyana cewa ₦40 za a riƙa biya kowace rana akan kowace gawa.
“Haraji ne ba na kai tsaye ba da masu gidajen ajiye gawa za su rika biya ba wai iyalin mamaci ba kuma ₦40 ne kawai ba ₦40,000 ba tun lokaci da aka fito da harajin babu wanda aka hana binne gawarsa,” ya ce.
“Hakan na nufin idan gawa ta yi kwana 100 ana sa ran gidan ajiye gawar zai biya gwamnati ₦4000.”