[ad_1]
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana gwamnati mai ci da shugaba Buhari yake jagoranta a matsayin gwamnatin makaryata.
Toshon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da yakewa mambobin jam’iyar PDP jawabi a Enugu.
Mai neman tsayawa takarar shugaban kasar ya ce jam’iyar APC ta yi alkawarin samar da ayyukan yi miliyan uku a kowace shekara amma ƙasar nan kullum karuwar rashin aikin yi ake samu da ya jawo mummunan rashin tsaro.
“Wannan gwamnatin, gwamnati ce ta makaryata sun yi alkawarin samar da ayyukan yi miliyan uku a shekara amma yan Najeriya suna rasa ayyukan yi miliyan uku a kowace shekara,”ya ce.
“Wannan rasa ayyuka ya haifar da mummunan yanayin rashin tsaro, Najeriya na cikin wani yanayi mai dauke da kalubale. A yau tattalin arziki na cikin mawuyacin hali kalubale mafi girma shine na rashin aikin yi.”
[ad_2]