Gwamnatin Borno ta yi alƙawarin kammala wasu gidajen ƴan gudun hijira

Gwamna Babagana Zulum na Borno ya tabbatar wa mutanen Logumani da Gajibo da suka rasa matsugunansu cewa nan ba da jimawa ba za a sake mayar da su zuwa yankunansu.

In ba a manta ba, ‘yan Boko Haram sun lalata muhallan al’ummomin biyu a ƙananan hukumomin Ngala da Dikwa, tare da raba ɗaiɗaita yankin tun shekarar 2014.

Sai dai gwamnan ya yi musu albishir, inda ya ce nan ba da jimawa ba za su koma gidajensu bayan kammala ayyukan gina gidaje 1,000 da ake yi.

Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake duba yadda aikin ke gudana a ranar Juma’a.

Ya ce yana da yakinin cewa za a kammala aikin kuma za a sake mayar da mutane nan da watanni biyu.

More from this stream

Recomended