Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Uba Sani ya yi alƙawarin sauya fasalin dukkanin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 255 dake jihar tare da daga darajarsu zuwa mataki na 2 a wani ɓangare na shirin da gwamnatinsa take na kawo gagarumin sauyi a fannin kiwon lafiya.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa cibiyoyin da aka daga darajarsu za su rika kula da masu cutar ciwon suga da bata tazzara ba, hawan jini, farfaɗo da masu ciwon cutar asima da kuma karɓar haihuwa da sauran ayyuka da suka kamata.
Uba Sani ya bayyana haka ne a Kachia a wurin bikin kaddamar da rabon magunguna kyauta da kayayyakin asibiti ga dukkanin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko dake ƙananan hukumomin jihar 23.
Ya ce an yanzu haka cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko 255 dake jihar sun fi na ko’ina inganci a dukkanin faɗin Najeriya kuma gwamnatinsa tana son jihar Kaduna ta cigaba da zama akan gaba a fannin lafiya a jihohin Najeriya.
Ya kuma yi nuni da cewa waɗanda za su ci moriyar maganin kyauta sun haɗa da kananan yara masu shekara 1-5, mata masu ciki sai kuma masu ƙaramin ƙarfi.