Gwamnan Zamfara ya ziyarci wasu al’ummomi da yan bindiga ke yawan kai wa hare-hare

Gwamnan jihar Zamfara, Mallam Dauda Lawal Dare  ya ziyarci wasu al’ummomi dake karamar hukumar Kauran Namoda biyo bayan  hare-haren da yan bindiga ke yawan kai musu.

Wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta ta Zamfara Circle Community Initiative ta fitar ya ce mutane 24 aka kashe a yayin da aka yi garkuwa da mutane 144 aka kuma jikkata 16 a kananan hukumomin da dama dake fadin jihar.

A watan Yuli an bada rahoton cewa yan bindiga sun kashe mutane 33 a kauyen Banga  su ka kuma  yi garkuwa da wasu bayan da suka karbi miliyan 30 a matsayin kudin fansa.

Da yake magana a ranar Laraba a yayin ziyarar gwamnan ya yi wa iyalan wadanda abun ya shafa ta’aziya inda ya ci alwashin kara korari a yaki da matsalar tsaro a jihar.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya tona asiri da kuma kunyata wadanda suke da alhakin mummunan hare-haren da kuma kashe marasa kan gado a jihar.

Ya ce ana kai hare-haren ne domin jefa tsoro a zukatan al’umma inda ya shawarce su da suka kara dagewa da addu’a.

Ya yi alkawarin bunkasa tituna, samar  da ruwan sha, wutar lantarki a yankunan da abun ya shafa.

Mai martaba Sarkin Kauran Namoda, Sanusi Ahmad ya yabawa gwamnan kan ziyarar da ya kai da kuma irin kokarin da yake wajen shawo kan matsalar tsaron

Al’ummomin da gwamnan ya ziyartan sun hada da Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru da Tambarawa.

More from this stream

Recomended