Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar bisa nasarar da ya samu na zama dantakarar shugaban kasa a jam’iyar PDP.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Bala Dan Abu, ya fitar ranar Lahadi, Ishaku ya ce Atiku ya samu nasara saboda jajircewarsa da soyayya da yake da ita ta hidimtawa kasa.
Ishaku ya kuma yabawa sauran shugabannin jam’iyar da kuma daleget kan yadda taron ya gudana cikin gaskiya da adalci.
Gwamnan ya kuma godewa sauran yan takara kan dattakon da suka nuna da kuma alkawarin da suka dauka na mara baya ga wanda ya lashe zaben.