Gwamnan Taraba ya karbi katin shiga jam’iyar APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya yi rijista a matsayin dan jam’iyar APC.

Kefas wanda ya karbi katinsa na jam’iyar a ranar Lahadi ya nuna godiyarsa kan kyakkyawar tarba da ya samu daga shugabannin jam’iyar ta APC dama mambobinta dake fadin jihar Taraba.

“Na karbi katina na jam’iyar APC daga hannun Hon Umaru Tanko shugaban jam’iyar APC na mazabar Hospital dake karamar hukumar Wukari l,” a cewar Kefas cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

An yiwa gwamnan rijistar shiga jam’iyar a gidan gwamnatin jihar dake Jalingo a wani gajeren biki da ya samu halartar manyan mutane ciki har da John Bonzena, shugaban majalisar dokokin jihar,Abel Diah, tsohon shugaban majalisar dokokin jihar da kuma Danladi  Baido jigo a jam’iyar ta APC Danladi.

More from this stream

Recomended