Gwamnan Taraba Ya Kai Ziyarar Fadar Shugaban Ƙasa Inda Ya Shiga Ganawar Sirri Da Tinubu

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kai ziyara fadar shugaban ƙasa a Abuja, inda ya shiga wata ganawar sirri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a safiyar Litinin.

Kefas ya isa Fadar Vila tare da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, abin da ya nuna cewar wannan ita ce ganawarsa ta farko da Tinubu tun bayan komawarsa daga PDP zuwa APC.

A kwanakin baya an shirya masa taron tarbar shiga jam’iyyar APC a ranar 19 ga Nuwamba, amma ya dage bikin sakamakon harin sace ’yan makaranta mata a Maga, Jihar Kebbi, inda ya bayyana cewa bai dace a yi shagulgula a lokacin tashin hankali ba.

More from this stream

Recomended