Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Uba Sani, ya sanar da rage kudin makaranta na dukkanin manyan makarantun jihar.
Gwamnan ya sanar da haka a lokacin wani taro da yan jarida a gidan gwamnatin jihar dake Kaduna.
A cewar, Muhammad Lawal Shehu mai magana da yawun gwamnan ya rage kudin makarantar ne domin cika alkawarin yakin neman zabe da gwamna Uba Sani ya yi wa al’ummar jihar Kaduna.
Ya ce an dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen jama’a kan tsadar kudin makarantar da yadda yake shafar yawan daliban dake shiga makarantun da kuma wadanda suke dorewa da karatun bayan sun shiga ciki.