Gwamnan Filato, Mutfwang ya koma jam’iyyar APC

Gwamnan jihar Filato,Caleb Mutfwang ya karbi katin shiga jam’iyar APC bayan da ya fice daga jam’iyarsa ta PDP.

Mutfwang ya karbi katinsa na jam’iyar APC a ranarĀ  Juma’a a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar da aka yi a Jos babban birnin jihar.

Gwaman ya ce bukatar samar da ingantaccen shugabanci,alkiblar da ta dace da kuma saita jihar Filato ta yi dai-dai da shirye-shirye da tsare-tsaren gwamnatin tarayya ne ya saka shi daukar matakin sauya shekar zuwa jam’iyar APC.

Mutfwang ya godewa jam’iyar PDP kan damar da ta bashi har ya lashe  zaben gwamnan jihar a shekarar 2023 da kuma goyon bayan da yan jam’iyar suka ba shi har ya zuwa wannan lokacin.

More from this stream

Recomended