Gwamnan Adamawa ya fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Umar Fintiri ya fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 kamar yadda gwamnatin tarayya ta amince.

Ƴan makonnin da suka gabata ne shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanya hannu kan dokar biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Tinubu ya sanya hannu kan dokar ne biyo bayan tirka-tirkar da aka sha da shuwagabannin kungiyar ƙwadago kan batun ƙarin na mafi ƙarancin albashin.

Amma kuma gwamnoni da dama sunce baza su iya biyan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba sakamakon yanayin matsin tattalin arziki da ake ciki.

Duk da haka gwamnan jihar ta Adamawa ya fara biyan ma’aikatan jihar mafi ƙarancin albashin daga watan Agusta tare da yin alƙawarin fara biyan ma’aikatan ƙananan hukumomi daga watan Satumba.

Hakan ya sa ma’aikatan sun shiga matuƙar murna da farin ciki.

Wasu ma’aikatan jihar da suka karɓi albashinsu  sun tabbatar da cewa sun samu ƙari.

More from this stream

Recomended