
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ziyarci Nnamdi Kanu shugaban kungiyar IPOB wanda ke zaman kaso a gidan gyara hali dake jihar Sokoto.
A watan da ya gabata ne babbar kotunĀ tarayya dake Abuja karkashin jagorancin mai shari’a, James Omotosho ta samu Kanu da aikata laifin ta’addanci inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Biyo bayan yankeĀ hukuncin ne gwamnan ya ce zai fara amfani da wani shiri da dabaru daĀ yake da su da zai kai ga an saki, Kanu.
Wani fefan bidiyo da aka wallafa a Facebook ya nuna yadda gwamnan ya kai ziyara gidan yarin dake Sokoto.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook lauyan Kanu,Ejimakor ya bayyana Otti a matsayin mutum mai faÉa da cikawa.
Ejimakor ya yabawa gwamnan kan yadda ya cika alkawarin da ya yi masa cewa zai ziyarci Kanu.
Kawo yanzu babu wata sanarwa da gwamnan ya fitar ko kuma daga gwamnatin jihar Sokoto da hukumar kula da gidajen gyaran hali kan ziyarar.

