Gwamnatin jihar Borno a kokarinta na ganin ta shawo kan matsalar tashin farashin kayayyakin abinci da kayayyakin more rayuwa, ta raba tireloli 20 dauke da shinkafa ga marasa galihu 35,000 a garin Monguno.
Gwamna Babagana Umara Zulum da kan sa ne ya jagoranci rabon kayayyakin, wanda Sanata Muhammad Tahir Monguno da wasu manyan jami’an gwamnati suka tallafa.
Tallafin na daga cikin kudirin gwamnatin jihar na rage radadin da ‘yan kasar ke ciki.
Kowane namijin da ya ci gajiyar shirin ya samu buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da wake, yayin da mata mazauna yankin suka samu tallafin kayan sawa da tallafin kudi N10,000.
Gwamna Zulum ya yabawa gwamnatin tarayya bisa goyon bayan da take bayarwa, yana mai cewa, “Mun yaba da yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da tausaya wa ‘yan kasarmu.”
Baya ga rabon shinkafar, gwamnatin jihar ta karbi tireloli 90 na taki, wanda za a raba wa manoma domin bunkasa noman abinci a fadin kasar nan.