Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya bayyana cewa zai rattaba hannu kan hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin bayar da bayanai ga ƴan bindiga, yana mai cewa irin waɗannan mutane ba su da gurbi a cikin al’umma mai wayewa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin wata ziyarar jaje da ya kai kauyen Zogirma da ke ƙaramar hukumar Bunza, inda ya yi ta’aziyya ga iyalan jami’an ‘yan sanda uku da aka kashe a wani harin da ake zargin ƴan bindigar Lakurawa ne suka kai.
Rahotannin da aka tattara sun nuna cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a a hanyar Zogirma zuwa Tilli, lokacin da ‘yan bindigar suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da matafiya, amma jami’an tsaro suka dakile su.
A musayar wuta da ta biyo baya, jami’an ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu, yayin da dama daga cikin ƴan bindigar suka hallaka.
“Ba za mu zauna kawai muna kallo ba yayin da maƙiya daga cikinmu ke cutar da mu,” in ji Gwamna Idris.
“Duk wanda aka tabbatar da laifinsa na ba wa ƴan bindiga bayani, zan sa hannu a kan takardar hukuncin kisa a cikin sa’o’i 24. Daure rayuwa ba hukunci bane mai tsauri a gare su.
“Irin waɗannan mutane abokan gaba ne na al’umma, dole ne su fuskanci hukuncin kisa,” in ji shi.
Gwamnan ya yi Allah-wadai da kisan jami’an tsaron, yana bayyana su a matsayin jarumai da suka rasa rayukansu wajen kare lafiyar jama’a.
Ya kuma sanar da tura karin jami’an tsaro zuwa yankin da kuma sauran wuraren da ke da hadari, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shugaban ƙaramar hukumar Bunza, Hon. Zayyanu Shehu, ya yaba da yadda gwamnan ya hanzarta kawo dauki, tare da bada tabbacin cewa za su ci gaba da goyon bayan duk wani yunkuri na inganta tsaro.
A nasa jawabin, Hakimin Zogirma, Alhaji Tijjani Muhammad, ya roƙi gwamnati da ta tabbatar da ci gaba da kasancewar jami’an tsaro a yankin, yana mai cewa harin da aka kai baya daɗi kuma ya firgita al’umma ƙwarai da gaske.
Gwamna Idris na Kebbi Ya Yi Alkawarin Hukuncin Kisa Ga Masu Bayar da Bayanan Sirri Wa ƴan Bindiga
